Sabon zababben Shugaban Kasar Amurka Joe Biden ya aike da wasika ga Shugaban Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya Volkan Bozkir inda ya bayyana zai yi aiki da Majalisar a fagen kasa da kasa.
Shugaban Zauren Majalisar Dinkin Duniya na 75 Volkan Bozkir ya yada wasikar da Biden ya aika masa ta shafinsa na Twitter.
A wasikar, Biden ya ja hankali game da cutar Corona (Covid-19), magance matsalar sauyin yanayi da matsalolin da ake fuskanta a yau a duniya, inda ya ce akwai bukatar hadin kan kasa da kasa don magance wadannan matsaloli da suka sha gaban duniya a yau.
Ya ce "Ina sauraren aiki da ku da Majalisar Dinkin Duniya game da matsaloli da damarmaki daban-daban wajen hadin kan kasa da kasa."