Zababben Shugaban Kasar Amurka Joe Biden ya zabi mutanen da zai yi aiki da su a matsayin masu magana da yawun Fadar White House wadanda dukkan su mata ne.
Sanarwar da Joe Biden ya fitar ta ce, wannan ne karo na farko a tarihin Amurka da dukkan masu magana da yawun Fadar White House za su zama mata, wadanda dukkan su suna da kwarewar aiki.
Biden ya ce "Wadannan mata na da matukar muhimmanci duba da yadda za su yi aikin kulla alakar sadarwa tsakanin Shugaban Kasa da jama'ar kasar, za a ba su amanar hada Amurkawa da Fadar White House."
Biden da Mataimakiyarsa Kamala Harris sun amince da nadin Jen Psaki a matsayin Kakakin Fadar White House.
Psaki ta yi aiki a zamanin Barack Obama a matsayin mataimakiyar daraktar yada labarai da kakakin Fadar.
Kate Bedinfield da yi aikin daraktar yakin neman zaben Biden, za ta zama daraktar yada labarai a Fadar House.
Daga cikin matan da aka nada don aiyukan sadarwaa White House har da Karine Jean-Pierre wadda za ta kasance mataimakiyar sakataren yada labarai, Pili Tobar kuma za ta kasance daraktan yada labarai ta Mataimakiyar Shugaban Kasa inda aka nada Ashley Etienne a matsayin mai bayar da shawara kan hulda da jama'a ga Harris.Haka zalika Biden ya nada Eizabeth Alexander a matsayin kakakin matarsa, Jill Biden.