Shugaban Kasar Amurka Joe Biden ya bayyana cewa, sun tattaunawa mai fa'ida da ma'ana tare da Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.
Shugaba Erdogan ya gana da takwaransa na Amurka a wajen taron Shugabannin Kasashe mambobin NATO da aka gudanar a Brussels Babban Birnin Beljiyom.
Bayan taron, Biden ya gudanar da taron manema labarai inda ya bayyana cewa, "Mun gana da Shugaba Erdogan, mun yi tattaunawa mai ma'amana da fa'ida."
Biden ya kara da cewa, a ganawarsu da Erdogan sun tattauna kan yadda za a samu cigaba kan batutuwa da dama.
Ya ce, "Jami'anmu za su ci gaba da tattaunawa, na yi imanin za a samu cigaba na gaskiya tsakanin Amurka da Turkiyya."