Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya ce bayanan karya game da sabon nau'in kwayar cutar Corona (Kovid-19) da rigakafinta a dandalin sada zumunta na Facebook suna yin sanadiyar mutuwar mutane.
Joe Biden ya yi bayani ga manema labarai game da ayyukan da ake gudanarwa don dakile annobar.
Dangane da zarge-zargen da ake yi cewa kafafen sada zumunta irin su Facebook na taka rawa wajen yada labaran karya game da alluran rigakafi da cutar, Biden ya ce:
"Cutar da muke fama da ita a halin yanzu ita ce daga cikin wadanda ba a yi musu allurar rigakafi ba. Suna kashe mutane,"
Jami'an kiwon lafiyar Amurka sun yi gargadin cewa hauhawar cutar da mace-macen da ake yawan samu na faruwa ne a yankunan da basu yi allurar ruga-kafin Korona ba.
Kakakin fadar White House Jen Psaki ita ma ta ce Facebook da sauran dandamali ba sa yin abin da ya kamata don yaki da labaran karya game da rigakafin Korona.
Mai magana da yawun Facebook Kevin McAlister ya bayyana cewa kamfanin ba zai damu da zarge-zargen da ake yi wasu wadanda basu da hujja ba.
Kamfanin ya fada a wata sanarwa ta daban da cewa,
"Mun cire sama da miliyan 18 na bayanan karya game da COVID-19 da kuma wasu labarai masu alaka da karyata kaidojin yaki da Korona.