Biden da Trump sun sha alwashin miƙa mulki ba tare da matsala ba

Biden da Trump sun sha alwashin miƙa mulki ba tare da matsala ba

Shugabannin biyu sun zauna a kusa da juna a gaban garwashin wuta mai ruruwa a cikin ofishin shugaban ƙasa, wani yanayi da ke alamta kwanciyar hankali, amma ƙunshe da tankiya da ke tsakaninsu.

Biden ya marabci Trump da sake dawowa fadar White House, inda ya kuma taya shi murnar lashe zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana a ƙasar a kwanan  nan, yana mai shan alwashin miƙa mulki ba tare da mishkila ba.

Biden mai shekaru 81 ya doke  Trump a zaben shekarar 2020, amma kuma ya janye daga takarar shugaban ƙasa a wannan shekarar biyo bayan rashin kataɓus a muhawwarar ƴan takarar shugabancin ƙasa, ya kuma miƙa wa mataimakiyarsa, Kamala Harris takarar.

Ba a bai wa manema labarai damar yin ko da tambaya guda ba a yayin ganawar jagororin biyu, saboda an tura su waje duk da tambayoyin da su ka yi ta jefawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)