Shugaban kasar Amurka Joe Biden bai yi nadamar kiran takwaransa na Rasha “mai kisa “ ba kamar yadda fadar White House ta sanar.
Mai magana ya yawon fadar White House Jen Psaki ta bayyana cewa shugaba Biden ya bayar da amsa kai tsaye ga tambayar da aka yi masa kai tsaye.
Tana ishara ne ga tambayar da aka yi wa shugaba Biden akan cewa ko ya yi tunani akan kira Putin mai “kisa”
Biden ya bayyana cewa "Mhmm. Na yi, inda ya kara jan kunnen Putin da cewa zai iya gane kuskurensa bayan masu leken asirin Amurka sun gano cewa Putin ya dauki mataki yadda zaben da aka gudanar a watan Nuwamba zai taimakwa tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump.
Rasha dai ta musunta dukkanin zargin da ake yi mata na tayi katsa landan a zaben Amurka.