Bayanai game da 'yan gudun hijirar Siriya

Bayanai game da 'yan gudun hijirar Siriya

A Siriya, gwamnatin Bashar al-Assad ta tilasta wa iyalai 30 wadanda ke dauke da mutane 150 yin hijira daga wani gari a lardin Quneitra da ke kudancin kasar zuwa Idlib da ke karkashin ikon 'yan adawa a arewacin kasar.

Iyalan da suka rasa muhallinsu sun fara isa garin Bab ne a arewa maso gabashin Aleppo kuma daga can suka karasa zuwa Idlib da motar bas.

An sanya iyalan a gidajen da wasu kungiyoyi masu zaman kansu na Turkiyya suka gina a Idlib.

Dangane da bayanan da mai kula da shiga tsakani na Siriya, wanda ke gudanar da bincike kan bayanan hijira a Siriya ya fitar, gwamnatin Assad ta tura mutane sama da dubu 10 zuwa yankuna a arewacin kasar a watan Yulin 2018 a matsayin wani bangare na tilastawa mutane kaura daga Dera da Quneitra.


News Source:   ()