Bayan shekaru hudu da yunkurin juyin mulkin ranar 15 ga watan Yuli a Turkiyya

Bayan shekaru hudu da yunkurin juyin mulkin ranar 15 ga watan Yuli a Turkiyya

Ya zuwa yanzu shekaru hudu kenen suka wuce bayan yunkurin juyin mulkin da ‘ya’yan kungıyar ta’addar FETO suka yi yunkurin yi a ranar 15 ga watan Yulin shekarar 2016 wanda bai yi nasara ba.

 

Akan wannan maudu’in mun kasance tare da Dkt Murat Yeşiltaş daraktan harkokin tsaro a Gidauniyyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam wato SETA…

Akwai dalilai da dama da suka sanya juyin mülkin rashin yin nasara. Mafi girma daga cikinsu shi ne yadda al’umman kasar Turkiyya suka fita suka yi fito-na-fito da masu yunkurin juyin mülkin. Haka ya sanya rashin nasarar juyin mulkin; al’umma kuwa suka yi nasara. Haka kuma yadda karfin siyasa ya fi karfin yunkurin juyin mülki na daya daga cikin dalilin da ya haifar da rashin nasarar juyin mülki a kasar.  Bugu da kari, cacan baki tsakanin gwamnatin farara hula da dakarun kasar Turkiyya a ranar 27 ga watan Afirilun shekarar 2007 ya sanya ganin cewa dakarun kasar sun fara wuce gona da iri; lamarin da ya sanya aka dauki matakan kara karfafa siyasa da kuma kafa tarihi a dangantakar soja-siyasa a kasar.

Bayan ranar 15 ga watan Yuli, Turkiyya ta habaka abubuwanta da dama da suka hada dana ciki dana waje. Jin kadan bayan yunkurin juyin mulkin an dauki matakan kakkabe mambobin kungiyar ta’addar FETO daga kasar. Tun daga ma’aikatan tsaro har zuwa ma’aikatun lafiya, shari’a, da ilimi an karbe iko daga hannun wadanda keda alaka da kungiyar; da yawansu kuma an kamasu da laifi an kuma hukuntasu. Mafi muhinmanci daga cikin wadan nan sune wadanda aka kama daga cikin rundunar sojan kasar. Baya ga a rundunar sojin kasar an kuma fitar da wasu jami’an ‘yan sanda wadanda ke da alaka da kungiyar da dama daga aikinsu.

Matakan kwaskwarimar da aka yi wa sashen tsaron kasar Turkiyya bayan yunkurin juyin mulkin ranar 15 ga watan Yuli nada muhimmanci kwarai da gaske. A sashen tsaron kasar dake karkashin ma’aikatar harkokin cikin gida da kuma ma’aikatan tsaron kasar an sauya wadanda ke rike da mudafan iko da dama. An dai dauki dukkan wadannan matakan domin kauda mambobin FETO daga ma’aikatun kasar. Haka kuma an dauki matakan ci gaba da yaki da kungiyar ta’addar PKK da DEASH ta hanyar kaddamar da farmakan Garkuwar Firat da makamantansu da suka haifar da rage karfin kungiyar a yankunan.

 

Haka kuma matakan da aka dauka a cikin gida sun yi muhimmaci sosai wajen inganta siyasar kasar. Zaben raba gardamar da aka gudanar a ranar 16 ga watan Afirilun shekarar 2017 ya haifar da sauya tsarin mulkin Turkiyya daga ta jamhoriya zuwa ta tarayya.

 

Huldan Turkiyya da kasashen waje ya dan samu wani dan tankarda bayan yunkurin 15 ga watan Yuli. Kafin 15 ga watan Yuli dakarun da suke da karfi wajen kalubalantar kungiyoyin ta’addanci sun dan raunana a lokacin 15 ga watan Yuli, lamarin da ya sanya su sake daukar sabon salon yakar kungiyar ta’addar DEASH da PKK a yankunan Siriya da Iraki. Wadan nan farmakan sun haifar da bude wata shafi a lamurkan dake tsakanin Turkiyya da Siriya. A yayinda dakarun Turkiyya suka yi nasarar kaddamar da Farmakin Garkuwar Firat inda suka kalubalanci kungiyar DEASH sun kuma rage kwarin gwiwar kungiyar PKK a yammacin Firat. Bayan Farmakin Garkuwar Firat an kuma dauki matakan kalubalantar PKK kai tsaye inda a ranar 20 ga watan Janairun 2018 aka kaddamar farmaki a Afrin inda aka kori mambobin PKK daga yankin Afrin. Da hakan ne Turkiyya ta fara daukar gwababan matakai a Siriya. A Farmakin Tafkin Zaman Lafiya da aka fara a watan Oktoban shekarar 2019, Turkiyya ta yi nasarar dakatar da dukkanin yunkurin kungiyar PKK a gabashin Firat da kuma lalata yunkurinsu na kafa wata gwamnati a arewacin Siriya. Haka kuma Turkiyya ta kalubalanci gwamnatin Siriya a watan Maris din shekarar 2020 a yankin Idlib. Dukkan wadannan matakan an yi sune bisa tsarin diflomasiyar da Turkiyya ta dauka bayan yunkurin juyin mulkin 15 ga watan Yuli.

 

Daya daga cikin matakan na Turkiyya mai muhinmaci shi ne wanda ta dauka a Libiya. Turkiyya wacce ta zabi bin tafarkin diflomasiyya domin magance rikicin Libiya da ya-ki ya-ki cinyewa tun daga shekarar 2011 kawo yanzu, ta zabi tallafawa halastaciyyar gwamnatin Libiya da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa a ranar 4 ga watan Yulin shekarar 2019. Turkiyya ta yi hakan akan yarjejeniyar kalubalantar mayakan Haftar ‘yan tawaye masu yunkurin juyin mulki. A sabili da yarjejeniya da gwamnatin kasar ta yi da Turkiyya ne aka yi nasarar kange mayakan Haftar daga karbe ikon Tripoli.

A karshe dai, ranar 15 ga watan Yuli bai kasance ba face ranar da ya haifar da tangarda ga harkokin Turkiyya. Amma Turkiyya ta dauki matakan kara karfin gwiwarta ciki da waje. Sai dai wanan lamarin ya sanya makiyan Turkiyya kara hada kansu musanman yadda suka fara kalubalantar Turkiyya a matakanta a Gabas ta Tsakiya. A dayan barayin kuma, musamman tare da Amurka ta samu wasu tangardar da suka yi wuyar gyarawa bayan 15 ga watan Yulin.

Turkiyya ta fuskanci kalubale masu yawa bayan yunkurin juyin mulkin 15 ga watan Yulin shekarar 2016, sai dai bayan shekaru hudu da afkuwar hakan, matakan da ta dauka sun karfafata. Wannan karfin da ta samu sun kasance sa’an da suka inganta harkokin tsaro da huldanta da kasahen waje.

 

Wannan sharhin Dkt. Murat Yeşiltaş daraktan harkokin tsaro a Gidauniyyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam wato SETA dake nan Ankara babban birnin kasar Turkiyya…


News Source:   www.trt.net.tr