“Barazana ba zai taba karya gwiwar Turkiyya ba”

“Barazana ba zai taba karya gwiwar Turkiyya ba”

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Turkiyya Hami Aksoy ya bayyana cewa barazana ba zai karya gwiwar kasar Turkiyya ba.

Ya bayyana hakan ne domin mayar da martani ga bayanan shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da ya kira a kakkabawa Turkiyya takunkumi. Aksoy ya kara da cewa,

“Ya kamata Faransa ta bar hangin ruwan fako ta zo ga shirin gaskiya, ta kaddamar da tsarukan da hankali zasu iya dauka”

A kwanakin baya Macron ya yi kira a kakkabawa Turkiyya takunkumi inda ya zargi Ankara da laifin sabawa dokar iyakar kasa akan shiga hakkin yankin ruwan Tarayyar Turai tare da amfani da hydrocarbon a yankin Gabashin Mediterranean.


News Source:   ()