Bankin duniyar ya bayyana cewa ƙasashen da ke taimakawa wajen tattara kuɗaɗen lamuni sun bayar da kuɗin da ya kai dala biliyan 23 da miliyan 700 ga sashen kula da tattara kuɗin lamuni na bankin, da aka fi sani da IDA, adadin da ya zarta ainahin kuɗaɗen da aka buƙata na dala biliyan 23 da rabi don bayar da lamuni ga matalautan ƙasashe.
Kakakin bankin duniyar ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa adadin kuɗin da ƙasashen suka tattara ya zarta yawan kudin da tun farko bankin ya nema don rabawa matalautan ƙasashen a matsayin bashi yayin taron tattara kudin bayar da lamunin da ya gudana shekaru 3 da suka gabata.
Bankin duniya na amfani da irin wannan kuɗaɗe wajen bayar da bashinsu da zai bayar da damar ninkuwarsu zuwa aƙalla ruɓanye 4 kamar yadda makamancin kudin ya iya sanar da dala biliyan 93 a shekarar 2021.
Bayanai sun ce za a rarraba kuɗaɗen zuwa ƙasashe 78 da suke tsananin buƙatar lamunin kamar yadda shugaban bankin Ajay Banga ke cewa a wata sanarwa.
Ƙasashen da suka tattara kuɗaɗen bayar da lamunin sun ƙunshi Norway da Spain baya ga China da Turkey da kuma Korea ta kudu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI