An sanar da mutuwar majo Janar dın kasar Rasha da kuma raunanan wasu manyan sojojı uku sakamakon fashewar bam din da aka samar da hannu a Siriya.
Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ce ta fitar da sanarwar a rubuce inda ta bayyana cewa, a yayinda tawagar wasu sojojin Rasha ke kan hanayrsu ta dawowa daga garin Deyrizor dake Siriya wani bam din hannu da aka ajiye a gefen hanya ya tashi.
Fashewar bam din ya yi sanadiyar raunanan sojoji uku da kuma mutuwar wani sojan Rashan mai mukamin majo janar sanadiyar munanan raunukan da ya samu.