Fararen hula 2 sun rasa rayukansu, wasu 14 sun samu raunuka sakamakon fadowar wani bam kan wani gida da ke lardin Faryab na Afganistan.
Kakakin helkwatar 'yan sandan Faryab Kerim Yurish ya shaida cewa, 'yan ta'addar Taliban ne suka harba din ga jami'an tsaro, amma tsautsayi ya sanya shi fadowa kan gidan fararen hula.
Taliban ba ta ce komai ba game da lamarin.
Jami'an gwamnatin Afganistan sun tafi Katar don tattaunawar neman kawo zaman lafiya mai dorewa a kasar.