Mutane 43 suka rasa rayukansu sakamakon nitsewar wani jirgin ruwa dauke da bakin haure daga Tunisia a tekun Bahar Rum.
Kungiyar bada agaji ta Red Crescent ta kasar Tunusiya ta sanar da cewa jirgin ruwan dauke da bakin haure ba bisa ka'ida ba daga garin Zuvare da ke arewacin Libya, zuwa kasar Italiya, ya nitse a gabar ruwan Tunisia.
An bayyana cewa akalla bakin haure 43 ba bisa ka'ida ba suka rasa rayukansu a ibtila'in, sannan an ceto 84.
An sanar da cewa bakin hauren wadanda ba bisa ka'ida ba a jirgin ruwan sun fito ne daga kasashen Masar, Sudan, Eritrea da Bangladesh.