Bakin haure 100 sun mutu a tekun Bahar Rum

Bakin haure 100 sun mutu a tekun Bahar Rum

Bayanan farko da aka samu sun bayyana cewa, mutane 100 sun rasa rayukansu sakamakon kifewar jirgin ruwan roba da bakin haure suke ciki a tekun Bahar Rum.

Shafin Twitter na Kungiyar Yaki da Gudun Hijira ta Kasa da Kasa da ke da helkwatar a Geneva ya sanar da cewa, hatsarin ya afku a tsakiyar tekun Bahar Rum inda a kalla mutane 100 suka mutu.

Sanarwar da wata kungiyar bayar da agaji ta Faransa mai suna SOS da ta yi aikin ceton mutanen a Bahar Rum ya fitar ta ce,

"Bayan tsawon awanni na neman mutane, mun firgita sosai. Mun shaida yadda ma'aikatan Ocean Viking suka tono buraguzan jirgin ruwan roba a arewa maso-gabashin Tarabalus. An bayyana jirgin na dauke da mutane 130 kuma bashi da laifya."

SOS ta ce, a lokacin da jirgin ruwan Oceanic Viking ya je wajen an ga jikkunan mutane 10, kuma ba a samu ko da mutum 1 da rai ba.


News Source:   ()