Daraktan bayar da agajin gaggawa a Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO Mike Ryan ya bayyana cewa babu tabbacin za'a kawo karshen Korona a cikin shekarar 2021.
Babban Daraktan WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya gudanar da taro ta yanar gizo daga Geneva inda aka tattauna akan lamarin Covid-19.
Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa bayan makonni bakwai da aka samu raguwar kamuwa da cutar a makon da ya gabata kuma an samu karin yawan mutanen dake kamauwa da ita a fadin duniya.
Daraktan bayar da agajin gaggawa ta hukumar kuwa Mike Ryan ya bayyana cewa an yi riga Malam Masallaci idan aka bayyana cewa za'a kawo karshen annobar a shekarar 2021.
Sabili da haka ya yi kira da a ci gaba da daukar matakan hana yaduwar annobar.