Babu sauran guri da ke da tsaro a Gaza-UNRWA

Babu sauran guri da ke da tsaro a Gaza-UNRWA

Hukumar kula da ƴan gudun hijirar Falasɗinu ta majalisar ta ce a yanzu babu wani sauran waje da ya rage mai tsaro a Gaza.

Wannan na zuwa ne bayan da wani sabon harin Isra’ilan ya hallaka mutane 30 ciki hare da mata da ƙananan yara.

Hukumar ta ce lokaci yayi da ya kamata masu ruwa da tsaki su tabbatar da tsare makarantu da kuma asibitici don baiwa fararen hula tsaron da suke buƙata.

A jawabin da yayi mataimakin shugaban hukumar ta UNRWA Scott Anderson ya ce abin takaici ne yadda Isra’ila ke kai hare-hare har cikin makarantu da asibitoci guraren da fararen hula ke neman lafiya ko kuma mafaka.

Scott ya ce ya zama dole ɓangarorin da ke rikici da juna su mutunta yarjejeniyar tsare fararen hula a yaƙin da suke gwabzawa.

Idan mai saurare zai iya tunawa a baya-bayan nan ne Isra’ila ta haramtawa hukumar aiki daga cikin ƙasar a cewarta, ma’aikatan hukumar na da hannu a harin ranar 7 ga watan Octoban bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)