Babbar matatar man fetur ta Iraki ta fara aiki

Babbar matatar man fetur ta Iraki ta fara aiki

Baiji, babbar matatar man fetur a kasar Iraki, wacce hare-haren kungiyar ta'adda ta DAESH suka lalata a garin Salahaddin ta fara samarwa bayan shekaru 7.

A cewar rubutacciyar sanarwar da Ma'aikatar Man Fetur ta Iraki ta fitar, an kammala gyaran matatar man fetur ta Baiji.

A cikin sanarwar an bayyana cewar an fara samar da ganga dubu 70 na man fetur a kowace rana a Baiji, wacce ita ce matatar man fetur mafi girma a kasar.

An bayyana cewar matatar tana samar da ganga dubu 280 na man fetur a kowace rana kafin kungiyar ta'adda ta DAESH ta kai hare-hare kuma a yanzu an fara aikin kara adadin samarwa.

Kungiyar DAESH ce ta kwace matatar, wacce ke biyan bukatun man fetur na wani sashe na kasar, a watan Yunin 2014.

Baiji, wacce 'yan ta'adda suka lalata ta shiga karkashin ikon jami'an tsaron Iraki a shekarar 2015.

 

 


News Source:   ()