Babban limamin jami'ar Al-Azhar Sheikh Ahmed et-Tayyib dake Masar ya yi kira da a tallafawa "Kudus" a cikin harsuna 15 a shafukan sada zumunta.
Tayyib yayi bayani a shafinsa Facebook,
"Ina kira ga dukkan al'ummomi da shugabanninsu da su tallafawa al'ummar Falasdinu wadanda ake zalunta da kuma basu gudunmowa ta ko wace fanni domin kwato 'yancin kasarsu."
Tayyib, ya ci gaba da bayaninsa a cikin harsuna 15,
"Ya zama wajibi a dakatar da yakin kuma matukar ana son a samar da lumana ya kamata a daina kallon gefe guda kawai."
Tun daga ranar 10 ga Mayu, Falasdinawa 139, yara 39, mata 22, suka yi shahada yayin da Falasdinawa 950 suka jikkata a hare-haren da Isra’ila ta kai Zirin Gaza.