Harris ta sha wannan alwashi ne yayin taron menama labarai da ta kira a ranar Alhamis, jim kaɗan bayan ganawa da Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da ke ziyara a birnin Washington.
Kalaman mataimakiyar shugaban na Amurka dai alama ce da ke nuna wani muhimmin sauyi da ake shirin samu dangane da manufofin ƙasar a yaƙin Gaza.
A yayin da shugaba mai barin gado Joe Biden ke cigaba da ƙoƙarin ririta ɗorewar kyakkyawar alaƙa tsakaninsa da Fira Ministan Isra’ila, ga dukkanin alamu lamurra za su sauya zuwa nan gaba, la’akari da yadda Kamala Harris ta fito fili wajen matsin lamba gareshi kan buƙatar gaggauta kawo ƙarshen mummunan yanayin da Falasɗinawa ke ciki ta hanyar amincewa da ƙulla yarjejeniyar tsagaita wutar yaƙin da aka shafe sama da watanni bakwai ana yi a Gaza.
Harris ta kuma nanata buƙatar samar da ƙasar Falasɗinu, ɗaya daga cikin hanyoyin da aka daɗe da zaɓa domin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.
A dai ranar ta Alhamis Benjamin Netanyahu ya gana da shugaban Amurka Joe Biden a karin farko, tun bayan haɗuwar da suka yi a birnin Tel Avive, sa’o’i bayan farmakin da mayakan Hamas suka kai cikin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI