Ba za'a taba mantawa da zaluncin da Isra'ila ke yi ba

Ba za'a taba mantawa da zaluncin da Isra'ila ke yi ba

Daraktan harkokin sadarwa a fadar shugaban kasar Turkiyya Fahrettin Altun, ya bayyana cewa ba za'a taba mantawa da irin zaluncin da Isra'ila ta aikata ba.
Ya nanata cewa,

"Kamar yadda ake tunawa da haƙuri da adalci na kakanninmu ko da bayan ƙarni ɗaya ne, haka ba za a manta da zaluncin Isra'ila ba har bayan shekaru." 

Altun ya yada wani faifan bidiyon wata yarinya mai suna Eman Askar 'yar kasar Masar dake waken dake bayyana "Labarin Falasdinu", a shafinsa na Twitter.

Da yake bayyana cewa gaskiya ba ta canzawa, Altun ya ce, "Gaskiya tare da rai ita ce alama mafi karfi. Kamar dai yadda hakuri da adalcin kakanninmu suke a cikin zukatanmu hakan kuma ba za'a taba mantawa da irin cin zaluncin da Isra'ila ta aikata a yankin Falasdinu ba".


News Source:   ()