Gwamnatin Jamus ta ki amincewa da bukatar cin tarar wadanda suka yi rajista don karbar allurar riga-kafin sabon nau'in kwayar cutar corona amma ba su je karba ba kuma basu soke shi ba.
Kakakin gwamnatin Jamus, Steffen Seibert a taron manema labarai da aka gudanar a babban birnin Berlin ya yi kira ga jama'a da su je wurin yin allurar riga-kafin.
Ya ce “Ta wannan hanyar, ba kawai kan ka za ka kare ba har ma da dukkanmu daga wata mummunar cuta."
Seibert ya lura cewa gwamnati ba ta da shirin sanya takunkumi kan wadanda ba su je karbar allurar riga-kafin da suka yi wa rajista ba.
Shugaban kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta Jamus, Mario Czaja da wasu ‘yan siyasa sun bukaci a ci tara ga wadanda ba su je karbar allurar rigakafin da suka yi wa rajista ba.