Falasdinawa 24 ne suka yi Shahada yayinda wasu 24 suka jikkata sakamakon hare-haren da azzalumar kasar Isra'ila ta kai a Zirin Gaza.
Sanarwar da Ma'aikatar Lafiya dake Gaza ta fitar ta bayyana cewa, mutane 3 sun sake yin Shahada wanda ya kawo adadin wadanda suka yi Shahada zuwa 24.
Wani jami'in kungiyar farar hula ya shaida cewa, daga cikin mutane 3 da aka kashe a wani gida a yammacin Zirin Gaza akwai mace 1 da nakasasshe 1.
A baya Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta sanar da Shahadar mutane 21 da suka hada da yara kanana 9 tare da jikkatar wasu 95 sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai musu.
A daren ranar Litinin ne Isra'ila ta sanar da fara kai hare-hare a Zirin Gaza inda ta dinga kai hari ta sama, kuma ta harba makaman roka daga Gaza zuwa kudancin kasar.