Ķasar Azerbaijan ta bayyana ķudurinta na siyar jirage marasa matuka mallakar ķasar Turkiyya.
Ministan tsaron ķasar Azerbaijan janar Zakir Hasanov ya bayyanawa kafar talabijin din ķasar da cewa ana shirin tanadar sabbin makamai da jirage marasa matuka.
A yayinda aka tambayi ministan ko ķasar zata sayi makamai da jirage marasa matuka mallakar ķasar Turkiyya kasancewar irin nasarar da aka samu ta amfani dasu a Libiya da Siriya?
Ya kada baki ya ce ehh akwai shirin haka, sabili da Turkiyya na taimakawa sojojin kasarmu, kuma zata cigaba da hakan yana da kyau mu sayi makaman da sojojin kasarmu zasu yi amfani dasu da jirage marasa matuka daga Turkiyya.