Shugaban kasar Azerbaijan İlham Aliyev, ya sanar da cewa dakarun ķasarsa sun kubutar da birnin Fuzuli daga mamayar Armenia.
İlham Aliyev, dake jawabi ga alumman ķasar ya bayyana cewa hare haren da ake kaiwa ba zasu karya gwiwar Azerbaijan ba.
"Mu ba zamu kaiwa ko wani farar hula hari ba. Abubuwan da suka ayyanar laifi ne ga bil adama. Zamu hukunta su"
“Ita Armenia daga ina take samun makamai, wake siyar mata da wadan nan makaman, tana shigowa da makamai ne ta haramtacciyar hanya "
Ya kara da cewa mun kubutar da birnin Fuzuli daga mamayar Armenia kuma za'a fara kiran Sallah a yankin.
Da yake kira ga sojojin Armenia da su fice daga yankunan Azerbaijan ya kara da cewa da haka ne za'a kaddamar da yarjejeniyar tsagaita wuta kuma kowa ya sani cewa mun daura damarar kubutar da dukkanin yankunanmu daga hannun Armenia.