Azabaijan ta sanar da kashewa tare da jikkata sojojin Armeniya sama da 550 a arangamar da suka yi a daren Litinin din nan.
Ma'aikatar Tsaro ta Azabaijan ta fitar da sanarwar cewa, Armeniya da ta yi mummunar asara, ta kuma rasa tankokin yakinta 22 da sauran motoci masu sulke. Haka zalika an lalata igwa guda 15 da jiragen sama marasa matuki 18.
Sanarwar ta kara da cewar an kashe tare da jikkata sojoji makiya sama da 550. An rusa ma'ajiyar makamai 3 ta sojoji makiya.
An bayyana cewar an kwashe kwamandar sojojin sama ta farmakan kauyen Talish Laftanal Kanal Lernik Babayan, kuma sojojin da ke tare da ita sun tafka babbar asara.
Sanarwar ta ce "Sakamakon sojojin makiya da dama da suka jikkata ana fuskantar matsaloli a asibitocin gwamnati da na soji, ana samun matsala a ma'ajiyar jini. Kamar yadda ya ka a koyaushe, Armeniya na boye asarar da sojojinta suka yi ga jama'a."
A gefe guda Azabaijan ta gargadi Armeniya da ke ci gaba da kai wa yankunan fararen hula hari.
Ma'aikatar Tsaro ta Azabaijan ta ce tun safe Armeniya ta ke kai hari garin Terter, kuma suna gargadar Armeniyan a karo na karshe.
Shugaban kasar Azabaijan Ilham Aliyev ya bayyana cewar sun aiyana zaburarwa a wani bangare na kasar.
A karkashin matakin da shugaban ya sanyawa hannu, za a dauki sojoji da za su yi yaki, kuma za a dauki sabbin matakan aiyukan soji.
Aliyev ya mika dukkan matakan da za a dauka ga Majalisar Ministoci ta Azabaijan.