Dakarun sojin Azabaijan a rana ta 8 da fara kai farmakai don kwato yankunansu da aka mamaye, sun kubutar da garin Jabra'il tare da wasu karin kauyuka 8.
Dakarun na Azabaijan da suka lalata motoci masu sulke da dama na Armeniya, sun kuma kwace makamai da yawa daga hannunsu.
Sojojin Azabaijan kuma a daren Litinin din nan sun kai hari da makami mai linzami a garin Mingechevir da yankin Absheron da ke Azabaijan.
Mai ba wa Shugaban Kasar Azabaijan shawara Hikmet Haciyev ya sanar da cewa kai hari da Armeniya ta yi zuwa garin Mingechevir da ake da kamfanunnuka da cibiyar samar da lantarki, na nuni da yadda ta kidime tare da rasa me za ta yi.
A wata sanarwar da Haciyev ya sake fitarwa ta shafinsa na Twitter ya ce sojoji na Armeniya sun kuma kai hari da makami mai linzami mai tafiyar kilomita 300 zuwa yankin Absheron.
Mutum 1 ya rasa ransa, wasu 32 sun jikkata sakamakon harin na makami mai linzami samfurin Smerch. A lardin Beylegan mutane 2, wa lardin Aacebedi kuma wani yaro mai shekru 14 ya rasa ransa sakamakon harin makami mai linzami.