Australia za ta ci gaba da amfani da allurar rigakafin Korona samfarin AstraZeneca

Kasar Australia ta bayyana cewa za ta ci gaba da amfani da allurar riga-kafin Korona samfarin AstraZeneca.

Hukumar Kula da Ingancin Kayayyakin kasar ta (TGA) ta bayyana cewa ba ta samu rahoto ko korafin matsalar jini bayan yin allurar riga-kafin Korona samfarin AstraZeneca a kasar ba.

Sanarwar ta kara da cewa  “Muna masu bayar da shwara ga al’umman kasarmu da su ci gaba da zuwa ana yi musu allurar riga-kafin Koronan”

An dai dakatar da amfani da allura riga-kafin Koronan samfarin AstraZeneca a kasashen nahiyar Turai da dama bayan samun rahoton daskarar da jini.

Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO ta kalubalanci lamarin inda ta bayyana cewa allurar ba ta da wata cutarwa kuma mafaninta sun fi matsalolinta yawa.

 


News Source:   ()