Ƙasashen Turai na duba yuwar sake ƙaƙaba wa Rasha wasu sabbin takunkumai

Ƙasashen Turai na duba yuwar sake ƙaƙaba wa Rasha wasu sabbin takunkumai

Tattaunawa domin daukar wannan mataki yanzu haka na gudana a tsakanin jakadu da kuma jami'an diflomasiya daga ƙasashen Turai, domin ganin sun ƙara tirsasawa ƙasar Rasha dangane da yakin da ta kaddamar a kan Ukraine.

Daga cikin ɓangarorin da suke tininin sanya sabbin takunkumin sun haɗa da ɓangaren safarar kayayaykin da ake kai wa Rashar da kuma takaita yadda ƙasar ke fitar da man ta zuwa ƙasashen duniya.

Rahotanni sun ce daga cikin tattaunawar da suke harda batun kaddarorin da aka rufe a babban Bankin Rasha da sabunta takunkumin da yanzu haka ke kan ƙasar.

Bayanai sun ce jakadun kuma na duba yiwuwar amfani da jami'an kwastam wajen tare duk wasu kayayaykin fito da ke tinkarar yankin.

Tom Keatinge na Cibiyar Turai ya ce, muddin Trump ya janye takunkumin da Amurka ta dorawa Rasha, ya zama wajibi ƙasashen Turai su zafafa na su domin biyan buƙatar da suke so.

Mai magana da yawun ofishin yakin neman zaɓen Trump ya ce matakai marasa ingancin da Joe Biden ke dauka sun daɗa ƙarfafa abokan gabar su, wanda ya kai ga yakin Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)