A wata sanarwa da Iran ta fitar, ta tabbatar da harin na yau Asabar, sai dai shalkwatar tsaron ƙasar ta ce ta samu nasarar tare da dama daga cikinsu, lamarin da ya takaita ɓarnar da suka yi, duk da cewa ta tabbatar da mutuwar sojojin ƙasar biyu.
Ga martanin da wasu ƙasashe suka maida kan harin:
Amurka
Kakakin Majalisar Tsaron Amurka Sean Savett ya shaidawa manema labarai cewa, Amurka batada hannu a wannan hari, inda ya ce sun maida hankali ne wajen warware rikicin Gabas ta Tsakiya ta hanyar difulomasiya.
Don haka ya ce kada Iran ta maida martani kan harin don kawo ƙarshen barzanar bazuwar yakin a yankin.
Birtaniya
Faraministan Birtaniya Keir Starmer ya ce Isra’ila na da hakkin kare kanta daga hare-haren Iran, sai dai shima ya ce kar Iran ta maida martani ta hanyar kai wani sabon hari.
Saudiya
Saudiya ta yi tir da harin da Isra’ila ta kai wa Iran wanda ta ce ya sabawa dokokin ƙasa da ƙasa.
A wata sanarwar da ma’aikatar kula da harkokin wajen ƙasar ta fitar, ta buƙuci dukkanin ɓangarorin su dakatar da kai wa juna hare-hare don dakatar da barzanar bazuwar rikicin.
Iraq
Ofishin faraministan Iraqi ya fidda wata sanarwa da yi Allah wadai da harin na Isra’ila, inda ta ce tana nan kan bakarta na ganin an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da kuma Lebanon, don samar da dai-daito a yankin.
Pakistan
Ma’aikatar kula da harkokin wajen Pakistan, ta yi tir da harin na Isra’ila kuma a cewarta ya saɓawa dokokin Majalisar Ɗinkin Duniya.
Sanarwar ta ce hare-haren da Isra’ila ke kaiwa na ƙara haifar da barzanar bazuwar yaki a yankin Gabas ta Tsakiya, inda ta buƙaci Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya gudanar da aikinsa wajen tabbatar da tsaro a yankin.
Hadaddiyar Daular Larabawa
Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce hare-haren na Isra’ila na ƙara haifar da baraza ga zaman lafiyar yankin Gabas ta Tsakiya.
A sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta fitar, ta jaddada muhimmancin kauda kai don kawo ƙarshen rikicin.
Oman
Ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta ce harin na Isra’ila ya saba wa dokokin ƙasa da ƙasa, sannan ta buƙaci ƙasashe su tashi tsaye wajen hana Isra'ilab kaiwa ƙashen da ke makwabtaka ta ita hari.
Malaysia
Malaysia ta bi sahul sauran ƙasashen wajen yin Allah wadai da harin, tare da bayyana shi a matsayin wanda zai ƙara rura wutar rikicin yankin baki daya.
Hamas
Itama ƙungiyar Hamas ta yi Allah wadai da harin na Isra’ila kan Iran, wanda ta ce ke haifar da barazana ga tsaro da kuma al’ummar yankin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI