Ƙasashen Mexico da Canada sun sha alwashin tsaurara haraji kan kayayyakin Amurka

Ƙasashen Mexico da Canada sun sha alwashin tsaurara haraji kan kayayyakin Amurka

A  ƙarshen mako ne shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan wasu sabbin haraje-haraje da zai ƙaƙabawa ƙasashen Mexico, Canada da China, inda ya bayyana su a matsayin waɗanda suka ci amanar ƙasarsa a wani yanayi da rikicin kasuwanci ya daɓaibaye ƙasashen da suka kasance masu alaƙar kut da kut da juna.

Trump ya faɗa a shafukansa na sada zumunta cewa , harajin ya zama dole saboda kare Amurkawa, ta hanyar tirsasawa ƙasashen biyan haraji kan kayayyakin da suke shigarwa ƙasar, kuma ya sha alwashin kawo ƙarshen shigowa Amurka da ƴan ƙasashen Canada da Mexico suke yi ta haramtacciyar hanya.

Trump ya kuma sanya dokar ta baci kan tattalin arziƙi, kaso 10 na haraji aka sanyawa kayyakin China, yayin da ƙasashen Mexico da Canada kuma aka sanya musu harajin kaso 25

Harajin zai haifar da hauhawar farashin kayayyaki abinda ake ganin zai kasance barazana ga yardar da Amurkawa suka bai wa Trump lokacin da suka zaɓe shi, wanda ya alƙawarta rage farashin kayan abinci, da na gidaje da kuma mai, da sufuri idan ya zama shugaban ƙasar.

Hakan ta sanya Trump ya bai wa Amurkawa haƙuri game da matsin tattalin arziƙi da za su fuskanta na ɗan gajeren lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)