
Trump ya ce Isra'ila za ta miƙa Gaza ga Amurka bayan ya bukaci sake tsugunar da al'ummar yankin a wasu wurare, lamarin da ya ce ba za a bukaci sojojin Amurka a yankin ba.
Ministan tsaron kasar Isra'ila, Israel Katz, ya umarci sojojin kasar da su shirya ficewar Falasdinawan da ke zaune a Gaza, amma bisa raɗin kansu.
Hare-haren da Isra'ila ta ƙaddamar kan Falasdinawa a Gaza, ya yi sanadiyar mutuwar mutane 47,583 tare da jikkata wasu 111,633.
Sai dai, rahoton ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza, ya bayyana adadin wadanda suka mutu zuwa mutum 61,709, yana mai cewa dubban mutanen da suka bace a halin yanzu, ana kyautata zaton sun mutu.
Akalla mutum 1,139 ne aka kashe a Isra’ila yayin harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga Oktoban 2023, inda ta yi garkuwa da mutum sama da 200.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI