Ministan sadarwa da harkokin siyasa na kasar Libiya ya isa birnin Damascus a jiya Asabar domin ganawa da sabbin jami'an kasar ta Syria.
Bayan ganawar, Al-Lafi ya shaidawa manema labarai cewa, ya tattauna da sabbin jami'an kasar Siriya kan harkokin soji da tsaro a tsakanin kasashen biyu.
Walid Al-Lafi ya bayyana cewa muhimmancin ganawar itace zata baiwa bangarorin biyu wato Syria da Libya wani sabon shafi na tunkarar matsalolin tsaro a tsakaninsu musamman a wannan lokaci mai cike da ƙalubale.
Jami'an sauran ƙasashe da na Larabawa suna ta tururuwa zuwa kasar Syria bayan hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad tsohon shugaban Syria, tare da yin alkawarin hadin gwiwa, da ba da goyon bayan sake gina kasar da ta lalace, da mika mulki cikin lumana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI