Shugabannin ƙasashen na G20 da za su shafe kwanaki biyu suna tattaunawa tsakanin jiya Litinin da kuma yau Talata, za su fi mayar da hankali ne akan sauyin da za a gani na manufofin Amurka dangane da hulɗa tsakaninta da ƙasashe, sakamakon sabuwar gwamnatin shugaba mai jiran gado Donald Trump dake shirin fara aiki.
Batutuwan da suka haɗa da kasuwanci, Sauyin Yanayi, da kuma tsaro ne za su mamaye taron shugabannin na G20 a Brazil, lamurran da ake sa ran kai tsaye sabbin manufofin da shugaba Trump zai aiwatar za su yi tasiri kansu.
Yayin jawabin buɗe taro, shugaban Brazil mai masauƙin baƙi Lula da Silva, ya buƙaci haɗin kan takwarorinsa wajen kawo ƙarshen tasirin matsalar Ɗumamar Yanayi da kuma Talauci, matsalolin da ya ce tasirinsu bayyane yake a akasarin sassan duniya.
Dangane da Talauci da Yunwa kuwa, shugaba Lula ya ce matsalolin basu da alaƙa da ƙarancin abinci ko rashin kyawun yanayi, waɗanda ya ce an ƙirƙire su ne ta hanyar aiwatar da manufofi na siyasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI