Ƙasashen duniya sun fara mayar da martani akan kalaman Trump na ƙwace Gaza

Ƙasashen duniya sun fara mayar da martani akan kalaman Trump na ƙwace Gaza

Ƙasar Saudiya ta ce ba za ta ƙulla dangantaka da Israila ba idan har babu yankin Gaza, da hakan ke zama martani kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump da ya sha alwashin ƙwace Gaza.

A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Saudiya ta fitar yau Laraba, ta yi fatali da duk wani shiri na kwashe Falasɗinawan Gaza zuwa ƙasashe makwafta.

Yarima mai jiran gado, Prince Mohammed bin Salman ya ce sun tsaya kan maganarsu ta cewa basa goyon bayan Trump, kuma babu abinda zai sanya su sauya.

Baya ga haka, ƙasar China ta sanar da cewa ba ta amince da tilastawa Falasɗinawa barin yankunansu ba, kamar yadda mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Lin Jian ya bayyana.

Shi ma Fira Ministan Australia Anthony Albanese ya ce manufofin Gabas ta Tsakiya ba za su taɓa sauya wa ba, tuntuni sun amince da zaman Israila a matsayin ƙasa da kuma Gaza a karan kanta, a don haka basa goyon baya.

A gefe guda kuma shugaban Falasɗinawa Mahmud Abbas ya ce suna faɗa da babbar murya cewa ba su amince da tayin Donald Trump na ƙwace Gaza ba, inda ya ƙara da cewa ba zai taɓa yiwuwa a hana Falasdinawa ƴancin su ba.

Haka zalika, ƙungiyar Falasɗinawa ta mayar da martani ga Trump, inda ta bayyana ƙarara cewa ba ta goyon baya.

Babban sakaren ƙungiyar Husseini al-Sheikh ya ce ƴa ƴan ƙungiyar sun yi watsi da wannan buƙata ta kwashe su zuwa ƙasashe da ke maƙwaftaka dasu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)