A karon farko kenan da ake samun adadi mai yawa na wakilan ƙasashen duniya da ke ficewa daga zauren Majalisar Ɗinkin Duniya don ƙaurace wa sauraron jawabin Netanyahu.
Ƙasashen na duniya sun ɗauki matakin ficewar ne domin nuna adawarsu da abin da Isra'ila ke yi a Gaza da kuma Lebanon.
Netanyahu ya kuma ce, za su ci gaba da ragargazar Lebanon da Gaza har sai sun cimma burinsu.
Netanyahu ya ce, sai sun ga bayan ƙungiyar Hamas domin muddin ta ci gaba da rike madafun iko, za ta sake farfaɗowa tare da sake kitsa hare-hare kan Isra'ila a cewarsa.
Netanyahu ya gargaɗi Iran
A yayin jawabin nasa, firaministan na Isra'ila ya yi gargaɗin cewa, za su ƙaddamar wa Iran da hari muddin ta takale su.
Ina da sako ga azzaluman Tehran. Muddin kuka kai mana hari, za mu rama. Babu wani wuri a cikin Iran da Isra'ila ba za ta iya kai wa farmaki ba. Inji Netanyahu.
Kalamansa na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila ta kashe kimanin mutane dubu 1 da 500 a farmakin da ta kai cikin Lebanon da zummar ƙaƙƙaɓe mayakan Hezbollah, adadin da shi ne mafi muni da aka gani a baya-bayan nan a ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI