
Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ne ya wakilci wasu daga cikin tsaffin shugabannin na Afirka wajen yin wannan gargaɗi ga taron menama labaran da ya gudana, a yayin da ministocin kuɗin ƙasashen G20 ke ganawa a birnin Cape Town.
Obasanjo, wanda ke jagorantar shirin nema wa ƙasashen Afirka sauƙi daga nauyin bashin da yayi musu dabaibayi, ya ce kamata yayi a ce ƙasashe marasa ƙarfi su riƙa zuba maƙudan kuɗaɗe wajen inganta tsarin ilimi, da kiwon lafiya da wadatar abinci, amma a maimakon haka su na karkata kuɗaɗen ne wajen biyan basukan da ba za su iya kawarwa a nan kusa ba.
Ƙasashen da ake ƙoƙarin nemawa sassaucin biyan bashin sun fito ne daga nahiyoyin Afirka, da Asiya, da Kudancin Amurka da kuma yankin Carribean.
Wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ya ƙiyasta cewar, idan har aka yi wa ƙasashe marasa ƙarfi sassauci kan bashin da suke biya, to fa za su iya samun rarar kudin dala biliyan 80, kuɗaɗen da ko shakka babu za su amfani ƙasashe a ƙalla 31 da talauci ya yi wa katutu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI