Ƙasashe sun fara kiraye-kirayen tsagaita wuta a Syria bayan tsanantar yaƙi

Ƙasashe sun fara kiraye-kirayen tsagaita wuta a Syria bayan tsanantar yaƙi

Kiraye-kirayen manyan ƙasashen na zuwa a wani yanayi da yaƙin ya sake rincaɓewa yau Litinin bayan da jiragen yaƙin Syria da na Rasha suka yi wani luguden wuta kan ƴan tawayen jiya Lahadi a birnin Idlib inda shugaba Bashar al-Assad ke shan alwashin daƙile duk wani yunƙurin dawowar ƴan tawayen cikin Aleppo.

Aƙalla mutane 25 suka mutu a luguden wutar jiragen yaƙin na Syria da taimakon Sojin Rasha, ƙasar da ke da sansani na musamman a Damascus wanda da shi ne ta ke aiwatar da manufofinta a Afrika.

Yaƙin na Syria na ci gaba da tsananta tare da tayar da hankalin duniya, dai dai lokacin da ake fama da mabanbantan yaƙe-yaƙe kama daga na Isra’ila a Gaza da Lebanon da kuma wasu sassa na Syriyar baya da yaƙin Rasha da Ukraine, wanda tuni ya sanya kiraye-kirayen manyan ƙasashen don ganin lafawar yaƙin na Syria da ke ƙoƙarin dawowa bayan nasarar dakatar da shi a shekarar 2016.

A makon jiya ne ɓangarori masu rikici da juna suka fara kai wa junansu hare-hare a wani yanayi da mayaƙan ƴan tawayen Kurdawa ke neman damar kwashe ahalinsu daga Aleppo don kaucewa faɗawa rikicin tsakanin bangarorin biyu da basa ga maciji da juna.

Wasu bayanai sun ce tuni mayaƙan da ke samun goyon bayan Iran suka fara tururuwar shiga Syria daga Iraqi don taimakawa Sojin na Syria da tuni suka jigata daga mayaƙan ƴan tawaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)