Kai tsaye nasarar na nuna yadda Trump zai sake samun damar jagorantar White House na tsawon shekaru 4 masu zuwa wanda kuma ke mayar da shi shugaba na biyu da ya jagoranci ƙasar sau biyu a mabanbantan lokaci.
Shugaba Xi Jinping na China da Recep Tayyib Erdogan su ne na farko-farko da suka aike da saƙon taya murnar, inda Xi ya bayyana fatan samun kyakkyawar alaƙa ba tare da tarnaƙi ba tsakanin Beijing da Washington.
Sai shugaba Emmanuel Macron na Faransa wanda ke cewa a shirye ya ke ya yi aiki da Donald Trump kamar yadda suka yi a baya, yayinda Giorgia Meloni ta Italiya da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu suka taya Trump murna bisa sake dawowa da ya yi a shugabancin Amurka.
Shugaban gwamnatin Austria Karl Nehammer ya ce za su yi aiki da Donald Trump domin tunkarar ƙalubalen da duniya ke fuskanta.
A ɓangare guda Firaministan India Narendra Modi na India da Ola Sholz na Jamus da kuma shugaban ƙungiyar tsaro ta NATO taya murna suka yi tare da fatan samun alaƙa mai kyau tsakaninsu da Amurka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI