Fiye da wakilcin ƙasashe 70 da ƙungiyoyi baya ga ƴan fafutukar yaƙi da matsalar ɗumamar yanayi ne yanzu haka suka hallara a birnin Baku fadar gwamnatin Azerbaijan don halartar taron na COP29 wanda ya faro a yau Litinin ake kuma fatan kammala shi ranar 22 ga watan nan.
Ana saran taron ya mayar da hankali kan barazanar da ke tunƙaro duniya bayan hasashen masana da ke gargaɗin cewa ana tunƙarar wani yanayi da ka iya zama mafi ƙololuwar zafin da duniya za ta fuskanta.
Taron na birnin Baku zai ja hankali ƙasashen don ci gaba da kasancewa a dunƙule wajen tunƙarar manufofin da ake fatan cimmawa a bangaren yaƙi da matsalar ta ɗumamar yanayi duk da matsalar da ka iya kunno kai daga zaɓaɓɓen shugaban Amurka.
Tuni dai zaɓaɓɓen shugaban na Amurka Donald Trump ya sha alwashin fitar da ƙasar ta shi daga yarjejeniyar yanayi ta birnin Paris wadda ke da nufin rage tiriri mai guba da ke haddasa ɗumamar yanayi daga ƙasashe masu manyan masana’antu.
Shugaban hukumar yaƙi da ɗumamar yanayi ta Majalisar ɗinkin duniyar Simon Stiell ya ce lokaci ya yi da ya kamata haɗakarsu ta yi aiki sosai don ƙalubalantar duk wata barazanar Trump ga ƙoƙarin na yaƙi da ɗumamar yanayi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI