Tun bayan sanar da kwace iko da birnin Damascus da ƴan tawayen Syria suka yi dai, ƙasashe da ƙungiyoyi na ƙasa da ƙasa suka fara bayyana matsayarsu kan wannan lamari.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta bakin jakadanta a ƙasar Geir Pedersen, ya ce abu mai muhimmanci a yanzu shi ne samar da mafita ta siyasa ga ƙasar, ba wai irin wacce aka yi amfani da ita a baya ba.
Ita kuwa a nata tsokacin, babbar jami’ar hulda da ƙasashen waje ta ƙungiyar Tarayyar Turai Kaja Kallas, ta ce wannan ne abinda dama suka daɗe suna fatan gani, wanda kuma ta ce ya kunyata Rasha da Iran da ke goyon bayan gwamnatin kama karya ta Al-Assad.
Suma dai shugabannin ƙasashen Faransa da Jamus da Isra’ila, bin sahun ƙungiyar EU suka yi wajen nuna farin cikinsu da kifar da gwamnatin Bashar al-Assad.
Tsohon shugaban Syria Bashar al-Assad. AFP - OMAR HAJ KADOURTo sai dai ra’ayi ya sha ban-ban da ƙasashe irinsu Masar da Lebanon da Yemen da Haɗaddiyar Daular Larabawa da Amurka, da suka ce za su ci gaba da sanya ido da kuma bibiyar lamuran da ke guna a ƙasar.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar kula da harkokin wajen Masar ta fitar, ta ce suna ci gaba da bibiyar lamuran da ke gudana Syria, kuma a shirye ta ke ta taimakawa wajen samar da haɗin kai tsakanin al’ummar ƙasar.
A nata tsokacin game da lamarin, Rasha da ke goyan bayan gwamnatin Al-Assad, ta ce ba kifar da gwamnatinsa aka yi ba, murabus ya yi da kansa bayan cimma matsaya da dukkanin ɓangarorin da abin ya shafa.
Shugaban Rasha Vladimir Putin tare da Bashar al-Assad. AP - Alexei DruzhininIta kuwa Qatar gargaɗi ta yi kan cewa kan a bari ƙasar ta faɗa cikin ruɗani bayan kawar da gwamnatin Assad.
Ministan harkokin wajen Turkiya Hakan Fida ya ce an samu sauyin gwamnati a Syria, kuma ba wai dare ɗaya hakan ta kasance ba, abu ne da aka kwashe tsawon shekaru 13 kafin samar da shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI