Ƙasashe masu tasowa sunyi turjiya kan tara dala biliyan dari 3 don yaƙi da sauyin yanayi

Ƙasashe masu tasowa sunyi turjiya kan tara dala biliyan dari 3 don yaƙi da sauyin yanayi

Bayan shafe aƙalla makwanni biyu ana kai ruwa rana tsakanin wakilcin ƙasashe 200 da suka halarci taron yanayi na COP29 a birnin Baku na Azerbaijan ne, aka cimma wannan matsaya bayan da dukkanin ƙasashe masu manyan masana’antu suka aminta da wannan kuɗi ko da ya ke ƙananun ƙasashen sun yi tirjiya.

Wakiliyar India a wajen taron Chandni Raina, ta ce waɗanan kuɗaɗe da aka amince za a bada ko kaɗan ba za su cimma muradun da aka sanya a gaba ba.

Shima ministan muhalli na Saliyo Jiwoh Abdulai, wanda ƙasarsa ke cikin matalauta a duniya, ya ce bisa la’akari da yawan kuɗin, ya nuna yadda manyan ƙasashe irinsu Amurka da Japan da sauran mambobin ƙungiyar tarayyar Turai, basu ɗauki abin da muhimmanci ba.

Dama dai suma gamayyar ƙasashen da ke kan tsuburi da masu tasowa da kuma wakilan Afrika, sun nuna rashin jin daɗinsu gama da matsayar da aka cimma.

Ƙasashe da dama sun zargi Ƙasar Azerbaijan, da ke fitar da man fetur da iskar gas, da rashin son cimma burin aka sanya a gaba akan lokaci, yayin da a yanzu tsananin zafi ke yiwa duniya barazana ta hanyar fuskantar ƙarin wasu bala'o'i.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)