A cewar wata sanarwa da ta fito daga fadar gwamnatin Faransa ta Elysee, ƙasashe 61 da suka amince da wannan ƙudiri sun haɗa da India, China da ita kanta Faransa.
Abin da ya bayyana ƙarara shi ne, Amurka da Birtaniya sun ƙi rattaba hannu a kan ƙudirin, su na mai nuni da muradan ƙasashensu da batun kiyaye ƙa’idoji.
Amincewa da wannan kudiri da gwamman ƙasashe suka yi na nuni da cewa a karon farko, an cimma matsaya a game da batutuwan da suka shafi fasahar AI da makamashi.
Waɗanda suka rattaba hannu a wannan ƙudiri sun jaddada muhimmancin ƙarfafa haɗin kai kan yadda ake tafiyar da fasahar AI, tare da hana wasu ƴan tsiraru mamayar fasahar domin kowa ya ci gajiyarta.
Duk da ta ƙi sanya hannu a wannan yarjejeniya, Amurka ta bayyana sha’awar haɗin kai ta ɓangaren fasahar AI,a yayin da ta ke gargaɗi a kan tsaurara ƙa’idoji da kuma hada kai da gwamnatocin kama-karya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI