Ƙasashe 52 sun buƙaci MDD ta sanyawa Isra'ila haramcin sayen makamai

Ƙasashe 52 sun buƙaci MDD ta sanyawa Isra'ila haramcin sayen makamai

Duk da yadda kiraye-kiraye ke ci gaba da tsananta wajen ganin Majalisar ta sanya dokar haramtawa Isra’ila sayen makaman, har yanzu ƙasashen Amurka da Jamus su ke matsayin ƴan gaba-gaba da ke wadata ƙasar da muggan makaman da ta ke amfani da su wajen kisan Falasɗinawa.

Zuwa yanzu ƙasashe 52 ne ƙarƙashin jagorancin Turkiya suka sanya hannu kan wata wasiƙar haɗaka da suka aike gaban kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin duniya wadda ke neman ganin an haramtawa Isra'ila sayen makamai, lura da yadda ta ke amfani da su wajen aikata kisan ƙare dangi kan Falasɗinawan da ke Gaza da yammacin gaɓar kogin Jordan.

Tuni dai kiraye-kiraye ya fara sanya wasu daga cikin ƙasashen da ke baiwa Isra’ila fara duba yanayin cikin makaman inda suka taƙaita wasu nau’in makamai da a baya suke sayarwa ƙasar cikin waɗanda ƙasashe har da Italiya da Japan da Spain wadda ta dakatar baki ɗaya kana Canada da ta rage yawan makaman sannan Netherlands da Belgium waɗanda suma suka rage makaman.

Sai dai har yanzu ƙasashe irin Amurka a kan gaba da Birtaniya da Faransa na ci gaba da aikewa da makaman a wani yanayi da Faransa ke muhawara kan yiwuwar taƙaita sayar da makaman ga Tel Aviv.

Kusan mutane dubu 50 Isra'ila ta kashe daga ranar 7 ga watan Oktoban bara kawo yanzu, inda ta faɗaɗa yaƙin da ta ke zuwa ƙasashen Lebanon da Syria da kuma Yemen a wani yanayi da ta kai mabanbantan hare-hare cikin Iran, lamarin da ya sake wargaza zaman lafiyar gabas ta tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)