Taron na COP16 da aka fara a jiya Litinin a birnin Cali da ke Colombia a ƙarƙashin jagorancin Majalisar Ɗinkin Duniya, zai mayar da hankali ne kan kyautatuwar alaƙar halittu masu rai da yanayin muhallinsu.
Ƙwararru da sauran masu ruwa da tsaki daga ƙasashe da dama za su yi tattaunawar ƙeke-da ƙeƙe akan nasarori da kuma gazawar da suka yi akan alƙawuran da suka ɗauka yayin makamancin taron da ya samu halartar ƙasashe 196 a birnin Montreal da ke Canada a shekarar 2022.
Daga cikin matakan bai wa halittu da muhallinsu kariya da taron na COP16 zai mayar da hankali kai, akwai alƙwuran da ƙasashe suka ɗauka na ware kaso 30 cikin 100 na fadin ƙasar da suke da shi domin samar da gandayen daji, sai janye tallafi ga dukkanin nau’ikan kasuwanci ko kamfanonin da ayyukansu ke yi wa muhalli illa, da kuma tilasta kamfanoni bayar da rahoton tasirin da ayyukansu ke yi akan muhallin. Dukkanin waɗannan alƙwura an ɗauke su ne shekaru biyu da suka gabata.
Tun a farkon taron bana ne dai ake sa ran ƙasashe su gabatar da shirye-shiryensu na bayar da kariya da kuma kyautata alaƙar hallitu da muhallin da suke rayuwa cikinsa, sai dai ya zuwa ranar Juma’ar da ta gabata, ƙasashe 31 daga cikin 195 suka cika wannan sharaɗi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI