Ya zuwa yanzu fararen hula 31 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-hare da makamai masu linzami da Armeniya ta kai Azabaijan.
Ofishin Gabatar da Kara na Azabaijan ya fitar da alkaluman rasa rayukan da aka yi a Azabaijan tun daga ranar 27 ga Satumba zuwa karfe 1 na ranar 8 ga Ootoba.
Sanarwar da aka fita ta ce a wannan lokaci an kashe fararen hula 'yan kasar Azabaijan 31, an jikkata wasu 154.
A hare-haren na Armeniya an lalata gidaje 973 da gine-gine gwamnati 133.
Mai Ba Wa Shugaban Kasar Azabaijan Shawara Hikmet Haciyev ya bayyana cewar an lalata wani makami mai linzami samfurin Grad da sojojin Armeniya suka harba unguwar fararen hula a Azabaijan.
Haciyev ya ce, tare da lalata Grad an kubutar da rayuwar fararen hula da dama.