Armeniya ta kai hari kan wata makaranta da ke hanyar Terter Agdam a kasar Azabaijan.
TRT ta nuna bidiyon makarantar da Armeniya ta kai wa hari a cikin Azabaijan.
Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta, Armeniya na ci gaba da kai hare-hare kannfararen hular Azabaijan.
Da safiyar Larabar nan sojojin Armeniya sun yi ruwan bama-bamai a yankin kasar Azabaijan inda suka jefa bam kan wata makaranta da ke hanyar Terter-Agdam.
TRT ta nuna bidiyon makarantar da aka lalata gaba daya.
Ya zuwa yau makarantu 13 ne Armeniya ta kai wa hari a yankin Terter.
Sojojin Armeniya na kai hari kan 'yan jaridu, fararen hula da gine-ginen gwamnati.
Sojojin Azabaijan sun kai hari kan motar 'yan jaridar tashar talabijin ta Azabaijan inda direbanta ha samu raunuka.
Ofishin Gabatar da Kara na Azabaijan ya ce daga 27 ga Satum a zuwa 14 ga Oktoba Armeniya ta kashe fararen hula 41 tare da jikkata wasu 206 a Azabaijan.
Sojojin Azabaijan da suka rasa yankunan da suka mamaye na kai hare-hare kan fararen hular Azabaijan.
Armeniya da Azabaijan sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Moscow babban birnin Rasha daga karfe 12.00 na ranar 10 ga Oktoba.
Tun ba a dauki awanni 24 da kulla yarjejeniyar ba Armeniya ta karya ta tare da kai harin garin Gence a ranar 11 ga Oktoba inda ta kashe fararen hula 9, ta kuma jikkata wasu 35.
A gefe guda kuma Azabaijan ta harbo jirgin yaki mara matuki na Armeniya.
Ma'aikatar Tsaro ta Azabaijan ta ce an harbo jirgin a yankin Fuzuli a lokacin da ya ke shawagi a sama.
A ranar 12 ga Oktoba ma Azabaijan ta harbo jiragen yaki marasa matuka na Armeniya guda 3.