Armeniya ta kai hari da makami mai linzami kan bututun mai na Baku-Tiflis-Ceyhan da ke kasar Azabaijan.
Sanarwar da Ofishin Gabatar da Kara na Azabaijan ya fitar ta ce, sojojin Armeniya dun kai hari kan bututun mai na Baku-Tiflis-Ceyhan da misalin karfe 9 na daren Talatar da ta gabata.
Sanarwar ta ce an kai harin a bangaren bututun da ke lardin Yevlah, kuma dakarun sojin Azabaijan sun kawar da harin.
Sanarwar ta kara da cewar bututun mai na Baku-Tiflis-Ceyhan na da matukar muhimmanci ga aiyukan samar da makamashi a Turai, kuma wannan hari da sojojin Armeniya suka kai hari ne na ta'addanci.