Sojojin Armenia sun sabawa yarjejeniyar tsagaita wutar da aka ayyanar tsakanin kasarsu da Azabaijan akan Nagorno-Karabakh.
Ma'aikatar Tsaron Azabaijan ce ta sanar da cewa, Armeniya ta aiwatar da ayyukan tsokana ta hanyar sabawa yarjejeniyar tsagaita wuta a yankunan Azabaijan da aka kubutar daga mamayarta.
A cikin sanarwar, an bayyana cewa Sojojin Azabaijan sun mayar da martanin da ya kamata kuma a halin yanzu suna cigaba da mutunta yarjejeniyar tsagaita wutan.
Nasarorin da sojojin Azabaijan suka samu a kokarin kubutar da yankunan Nagorno-Karabakh daga mamaya a ranar 27 ga watan Satumba ya tilasta wa Armenia sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar 10 ga Nuwamba.