Bayan an fitar da wani rahoton dake nuna kashe farar hula 39 da dakaru Australia suka yi aka fara kiraye-kiraye domin hukunta sauran sojojin kasashen waje da suka aikata laifukan yaki a kasar ta Afghanistan.
Mai fafutukan kare hakkin dan adam Nezamuddin Katawazi, ya bayyana cewa rahoton ya kamata ya zama wani dama da zai sanya a hukunta dukkanin dakarun kasashen waje da suka aikata laifuka a kasar Afghanistan.
Ya kuma shaidawa kanfanin dillancin labaran Anadolu da cewa "Yayinda muke mutunta matakan da ma’aikatar tsaron Australia ta dauka na hukunta mutun 19 da ake zargin sun aikata laifukan yaki a Afghanistan a tsakanin shekarar 2003 zuwa 2016, muna masu kira ga sauran kasashe su gudanar da bincike akan zarge-zargen da ake yiwa dakarun kasashensu na aikata laifuka yaki da cin zarafin bil adama a kasar da kuma hukunta dukkanin wadanda aka samu da laifin”