Anyi cacar baka tsakanin Macron da Netanyahu kan rikicin Gabas ta Tsakiya

Anyi cacar baka tsakanin Macron da Netanyahu kan rikicin Gabas ta Tsakiya

An jiyo Macron na bayyana matuƙar ɓacin ransa ga majalisar ministocinsa dangane yakin da Israilar ke yi, inda ya ce kada Netanyahu ya manta cewar ƙudirin Majalisar Ɗinkin Duniya ne ya kafa ƙasarsa, saboda haka bai dace ya dinga bijirewa ƙudirorin ta ba.

Macron na nuni ne ga ƙudiri na 181 da Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da shi a watan Nuwambar shekarar 1947 na raba ƙasar Falasdinu biyu wadda ta zama ɓangare guda na Yahudawa, ɗayan ɓangaren kuma na Larabawa.

Rahotanni sun ce Netanyahu ya kadu da waɗannan kalamai, inda yake cewa ya dace Faransa ta san cewa ba Majalisar Ɗinkin Duniya ce ta kafa ƙasar su ba, sai dai nasarar da suka samu a yaƙin neman ƴanci tare da sadaukar da jinin mayaƙan su, akasari waɗanda suka tsira daga kisan ƙare dangin da aka musu ciki harda na ƙarƙashin mulkin Sarki Vichy na Faransa.

Wannan cacar bakin na zuwa ne a daidai lokacin da Faransa ke ci gaba kiran tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Lebanon, tare da sukar hare haren da ya zarge ta da kai wa da gangan a kan dakarun samar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya, abinda ya kai ga jikkata wasu da dama.

Netanyahu ya sake jaddada matsayinsa na janye dakarun samar da zaman lafiyar daga kudancin Lebanon domin bai wa sojojin ƙasar damar ci gaba da kai hare hare Lebanon domin murkushe mayakan Hezbollah.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP ya ce a tatatunawar da shugabannin biyu suka yi ta waya, Netanyahu ya shaida wa Macron cewar ba zai amince da shirin tsagaita wuta ba, ba tare da sauya harkokin tsaron a ƙasar Lebanon ba, wadda ka iya komawa yadda take bayan wani lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)